Akalla wasiku uku ne jam’iyyar MPN Kishin Kasa, ta ce ta aikawa Firayim Ministan Nijar Birji Raffini a matsayinsa na kasancewa shugaban majalisar warware rigingimun siyasa akan bukatar gyara kurakuran dake cikin kundun tsarin zaben kasa da yadda tsarin wakilci yake a hukumar zabe.
To sai dai tunda suka aika da wasikar, shiru ka ke ji kamar an shuka dusa, saboda haka ne shugabannin jam’iyyar MPN suka fitar da wata sanarwar fadakar da duniya abun dake gudana.
Onarebul Masani Korone shi ne mataimakin shugaban jam’iyyar ta MPN, yana mai cewa sun yi magana a majalisa da wasu hukumomin da suka dace, sun rubuta wasiku amma ba’a basu amsa ba.
Jam’iyyar MPN, Kishin Kasa, tana da kujeru biyar a majalisar dokokin kasa saboda haka ta samu mukamai a gwamnatin hadin gwiwa da shugaba Issoufou Mahamadou ya kafa.
Korafin na jam’iyyar ya sa wasu na ganin alamar Baraka ce tsakanin kawancen dake mulkin kasar kodayake kakakinta Asumanu Muhammadou ya musanta zancen Baraka.
Shugabannin jam’iyyar sun nanata cewa zasu ci gaba da gwagwarmayar har sai sun ga abun da ya turewa buzu nadi.
Tuni dai matasan jam’iyyar suka goyi bayan matsayin uwar jam’yyar akan lamarin kamar yadda wani matashi Habila Rabiu ya tabbatar.
Ga rahoton Souley Barma da karin bayani
Your browser doesn’t support HTML5