Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahamadu Isuhu Ya Bayyana Samun Nasarori a Shekara Ta Biyu


Shugaban Nijar, Mahamadu Isuhu
Shugaban Nijar, Mahamadu Isuhu

Yayin da gwamnatin Mahamadu Isuhu na Jamhuriyar ta cika shekaru biyu a wa'adinsa na karshe, jami'an gwamnatin sun ce sun cika wasu daga cikin alkawuran da suka dauka a lokacin yakin neman zabe. Sai dai masu fafutuka na bayyana akasin hakan.

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar karkashin jagorancin Mahamadu Isuhu ta ce ta samar da ci gaba na a-zo-a-gani a kasar a wa'adinta na biyu.

A jiya Lahadi shugaba Isuhu ya bayyana a gidan talbijin inda ya zayyana ire-iren ci gaban da kasarsa ta samar yayin da ya cika shekaru biyu a wa’adinsu na biyu.

“Ga likitoci da aka samar a asibitoci daban-daban, musamman ma a Maradi da Yamai da kayayyakin aiki da aka samar a asibitocin, hakan ya sa a irin kididdigar da ake yi, an sa Nijar a cikin kasashen da ke kiyaye lafiyar al’umarta.” Inji Ministan raya al’adu kuma kakakin gwamnatin ta shugaba Isuhu, Asoumana Malam Isa.

Ya kara da cewa an samu ci gaba a fannin ilimi yana mai cewa “gano matsalolin da malamai ke da su” a fannin na ilimi “wannan ma ci gaba ne.”

Sai dai gwamnatin ta shugaba Isuhu ta amince da cewa akwai sauran matsaloli da kasar ke fuskanta, kamar na cin hanci da rashawa.

Sai dai kungiyoyin fararen hula na ganin akwai kurakurai da gwamnatin take tafkawa tun bayan da shugaba Isuhu ya samu wa’adi na biyu.

“Shi yana murna ya shekara biyu, mutane kuma suna bakin ciki ya yi shekara biyu yana muzguna masu.” Inji Jami’in fafutuka Gamatou Muhammadu.

Saurari cikakken rahoton Sule Mumuni Barma kan wannan batu:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:30 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG