Muhammad Chubado Babajiki darakta ne a hukumar da ke lura da harkokin sadarwa wato NCC. Masu sauraro zasu yi mamakin alakar harkar fina-finai da hukumar da ke lura da harkokin sadarwa duk da cewar dukkanin fim ma wata hanya ce ta isar da sako.
Muhammad Chubado ya ce hukumarsa ke da alhakin ba da rijista mussamam ga wadanda suke sanya fina-finai a fagen yanar gizo, a don haka dole a dama da hukumar NCC.
Ya ce suna tantance ire-iren wadannan fina-finai ne ta hanyar basu lasisi kuma kafin a basu wannan lasisi, sun san cewar a dole ne su bada fina-finan su domin a tantance kafin su fitar da wadannan fina-finan.
Idan aka yi rashin sa’ar cewar wadan nan fina-finan suka kubucewa hukumar na rashin bincikensu akan ci tararsu na rashin bin dokiki hukumar ko dai ta hanyar biyan tara na mafi karancin naira miliyan daya ko ma soke lasisin su gabaki daya.
Har ila yau Dandali ya tambaye shi ina batun saukaka masu sana’ar fina-finai musammam ma ta kafar internet, sai ya ce suna aiki akan haka domin ganin an saukakawa masu amfani da network a nan kusa ba da jimawa ba.
Ya ce a yanzun haka suna nazari na saukakawa da zasu baiwa kamfanonin da suke samar da data domin samun saukin aiki da ya dangance sadarwa.
Ga karin bayani a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5