‘Yan kasar Guinea Bissau suna dakon sakamakon zaben shugaban kasar zagaye na biyu, wanda tsoffin Firai Ministan kasar biyu suka fafata kana dukansu sun yi alkawarin dawo da kwanciyar hankali a fagen siyasan kasar.
WASHINGTON DC —
Zaben yana zuwa ne bayan shafe shekaru ana rikicin siyasa abinda ya hana karamar kasar da ke Afrika ta yamma ci gaba.
An dai buga a wannan zagayen a tsakanin tsoffin Firai Minista biyu wato Domingos Simoes Pereira da Umaro Cissoko Embalo.
Yayin da shekarar 2019 ta ke shirin karewa, ‘yan Guinea Bissau suna fatan wannan zaben da kuma sabon karnin da za a shiga zai samar da wani babi na sabon zaman lafiya a kasar.
Sakamakon farko na zaben za’a fitar da shi ne a gobe Laraba a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar.