Kungiyar ta bayyana a wani taro da ta yi cewa, akwai butakar bayyanawa 'yan Najeriya mutanen da aka ce suna kara hasasa matsalar tsaro musamman masu mu’amala da kudaden ketare su dari hudu da kungiyar tarayyar kasashen Larabawa ta zarga.
Kakakin kungiyar ta Middle Belt Forum, Dakta Isuwa Dogo yace taron ya tattauna batutuwan tsaro ne musamman a jihohin shiyyar tsakiyar Najeriya.
Shima shugaban kungiyar kananan kabilu a Arewacin Najeriya, Suleiman Sukukum yace hakkin gwamnati ne ta kare ‘yan kasa, amma idan ta gaza yin hakan, ya zamo dole mutane su nemi hanyoyin tsare kansu bisa ka’idar doka.
Kungiyar ta Middle Belt Forum ta kuma bukaci a samar da hukuma ta musamman da zata raya yankin da kawo karshen matsalolin tsaro a jihohin dake tsakiyar Najeriya.
Saurari rahoton Zainab Babaji cikin sauti:
Your browser doesn’t support HTML5