Al-Shabab Ta Kashe Sojojin Tarayyar Afirka Shida

Mayakan Kungiyar al-Shabab

Kungiyar al-Shabab ta kai harin bazata akan sojojin tarayyar Afika inda ta kashe shida ita kuma tayi asarar 11 a ramakon gayya.

Sojojin kungiyar tarayyar Africa su 6 ne aka kashe a hari daban-daban da kungiyar al-shabab ta kai a kudancin Somalia cikin awoyi 24.

KUNGIYAR DAKARUN TABBATAR DA TSARO TA TARAYYAR AFIRKA, wadda ake kira AMISON tace sojojin Burundi 3 ne kungiyar ta al-Shabab ta kashe a ranar Lahadi, lokacin da suka kaiwa tawagan sojojin harin ba zata a wani gari kusa da yakin lardin Shabalele, hakan kuma yayi sanadiyyar wasu sojojin da dama sun samu rauni.

Mai magana da yawun kungiyar ta al-Shabab yace sojoji biyar suka kashe.

Gwamnan jihar Shabalen Abdulkadir Mohammed Nur ya shaidawasashen Somaliya na Muryar Amurka cewa a kalla yan kungiyar na al-Shabab su 11 ne aka kashe sakamakon bude wa juna wuta da akayi dasu da sojojin na Somalia.

Ranar Asabar din data gabata ne kungiyar ta al-Shabab takai wa tawagar sojojin kasar Kenya harin ba zata ta kashe uku daga cikinsu tare da jima sojoji 8 rauni.

Daya daga cikin sojojin kasar Kenya ya shaidawa manema labarai cewa kungiyar ta al-shabab ta kai wa sojojin harin ba zata nea yankin Debio lokacin da suke sintiri. Yace an dauki wadanda suka samu rauni zuwa kasar Kenya cikin jirgin sama.