Al-Shabab A Somaliya Ta Kasu Gida Uku Kuma Da Alamun

Sojojin kiyaye zaman lafiya na Tarayyar Afirka suke sinitiri a yankunan da Al-Shabab ta bari

Babban Jakadan Majalisar Dinkin Duniya mai lura da al’amuran kasar Somalia jiya laraba, yake ambaton cewa an sami gagarumin sauyi a harkokin tsaron Somaliya musamman a Mogadishu.

Babban Jakadan Majalisar Dinkin Duniya mai lura da al’amuran kasar Somalia jiya laraba, yake ambaton cewa an sami gagarumin sauyi a harkokin tsaron Somaliya musamman a Mogadishu babban birnin Kasar tun daga lokacin da kungiyar al-Shabab ta bada sanarwar janye mayakanta daga birnin.

Jakada Aigistine Mahiga ya shaidawa taron manema labarai cewa matakain da al-shabab ta dauka da take cewa wai mataki ne na ja da baya wanda ba tsoro bane, amma ga dukkan alamun hakan yasa kungiyar al-Shabab ta sami rarrabauwa sannan ya kara da cewa:

Jakada Mahiga yana mai cewa rundunar kungiyar sai suka kasu kashi-kashi domin akwai bangaren da ya kama hanyar kudanci, wani bangaren kuma saiya nufi yammaci, gefe guda kuma sai wasu mayakan suka kama hanayar Arewaci, sassan duka suna kaiwa da komowa sun risa alkiblar bi. Hakan kuma ya wargaza karfin da rundunar al-Shabab ke dashi a lokacin da kanta ke hade a birnin Mogadishu.

Jakadan na Majalisar Dinkin Duniya a Somalia Augustine Mahiga yace rundunar hadin gwiwar Majalisar Dinkin Duniya da tarayyar Afirka sun gigita mayakan al-Shabab matuka gaya. Yace ganin yadda yanzu ita kanta rundar al-shabab din ke karancin kudi, sai goyon bayan da take samu ya ragu sosai a yankin gabas na tsakiya da kasashen yankin Arebiya.

Waje daya kuma kasuwar Bakaara ta sami komabaya, daman ribar da ake samu a kasuwar ce ke taimakawa tattalin arzikin yankin birnin Mogadishu, amma mamayewar da mayakan al-pshabab suka yiwa yankin ya kori ‘yan kasuwa da sukurkuta cinikayya.

Jakada Mahiga ya kuma yaba da takunkumin da kwamatin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya azawa al-Shabab domin hakan ya rage karfin rundunar sojin al-Shabab.Jakadan na MDD yace sauyin da aka samu a harkokin tsaron birnin Mogadishu na nufin baiwa MDD sukunin fadada ikonta zuwa wasu sassan kasar Somaliya kamar yadda yake cewa

Jakada Mahiga yana mai cewa tun farko sun dauka cewa za’a dauki tsahon akalla shekar guda kafin samun ingantuwar harkokin tsaron birnin Mogadishu, amma yanzu MDD ta sake sabon tsarin wajen shirya samun cikakken tsaron a gajeren lokaci, tare dafadada ayyukan ceto a dukkan sassan Somalia.