Akwai Sauran Rina a Kaba a Yaki Da Ta'addanci a Duniya - Bincike

Duk da manyan nasarorin da aka samu akan ‘yan kungiyar ta’addanci kamar na IS da al-Qaida har yanzu an gaza magance bazuwarsu a fadin duniya.

Wannan na daya daga cikin abin damuwar da aka gano kenan a wani sabon rahoto na gwamnatin Amurka game da ayyukan ta’addanci.

Binciken da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi akan ta’addanci, wanda aka fidda jiya Laraba, ya yaba da manyan nasarorin da aka samu a kokarin da Amurka ke yi na magance ta’addanci, duba da nasarar da aka samu wajen murkushe daular ‘yan kungiyar IS a Iraq da Syria, da kisan tsohon shugaban kungiyar IS Abu Bakr al-Baghdadi da kuma kisan Hamza bin Laden, dan Osama bin Laden wanda ya kirkiro kungiyar al-Qaida.

Sai dai har yanzu rahoton ya gano cewa duka wadannan nasarorin ba su isa ba.

Rahoton ya ce duk da nasarorin da aka samu, har yanzu ana ci gaba da fuskantar mummnar barazanar ‘yan ta’adda.