Akwai Mafita Ga Kowane Irin Kalubale Da Duniya Ke Fuskanta - Masana

Akwai Magani Ga Kowane Kalubale Sai Dai In Ba A Yi Amfani Da Shi ba - Masana.

Yayin da wasu kasashen duniya ke fuskantar kalubale ta fuskoki daban-daban, masana sun ce akwai mafita ga kowane irin kalubale da ake fuskanta a duniya.

Wannan na zuwa ne lokacin da masana ke ta karfafa gwiwar jama'a akan amfani da koyarwar magabata irin mujadaddi Shehu Usmanu Dan fodiyo da makamantansa, domin fita daga matsalolin da suka shafi jama'ar duniya.

Akwai Magani Ga Kowane Kalubale Sai Dai In Ba A Yi Amfani Da Shi ba - Masana

Da jimawa, masana ke tsokaci akan ayyukan magabata, wadanda suka samar da al'ummomi na gari wadanda suke rayuwa cikin zaman lafiya da yawa a sassa daban-daban na duniya.

Dokta Abdullah Hakeem Quick na cibiyar nazarin addinin musulunci ta Toronto dake Canada, na daga cikin masana da ke da'awar koyi da ayyukan magabata, wanda ya yi tsokaci akan fadi-tashi da sadaukarwa da shaihunan musulunci suka yi a duniya, inda ya karkata ga gudunmuwar Shehu Usman Dan fodiyo daga yankin Afirka.

Akwai Magani Ga Kowane Kalubale Sai Dai In Ba A Yi Amfani Da Shi ba - Masana

“Ana ambaton sunan Shehu Danfodiyo a fadin yankin Amurka, jama'a na karatun rubuce-rubucensa, kuma wannan dama ce garemu mu amfana da wannan babban malami, a cikin littafinsa na Ihya'us Sunnah, ya yi tsokaci akan yadda za'a magance matsalolin rayuwa da ke fuskantar jama'a, kuma shi ne abin da muke nema a yau, hakan ya nuna cewa koyarwarsa, tana amfani ko yaushe, ba a Amurka ba har ma ko'ina cikin duniya”

“Me ya sa muke jin za mu amfana da koyarwar Shehu Danfodiyo? Za mu amfana da ita saboda muna son sauyin rayuwa, muna son al'umma ta gari, domin ya kawar da munanan halaye cikin jama'a, ya gyara munanan dabi'u tsakanin musulmi da wadanda ba musulmi ba, ya kalubalanci zalunci tsakanin shugabanni, ya gyara tarbiya.”

Akwai Magani Ga Kowane Kalubale Sai Dai In Ba A Yi Amfani Da Shi ba - Masana

Masana na ganin da za'a yi amfani da wadannan ayyukan da makamantansu, za su iya zamowa magani ga matsalolin da suka shafi al'ummar yau.

Dokta Ahmad Gummi, wanda ke cikin masu wannan ra'ayin, ya ce akwai magani ga matsalolin da ke damun mu tun da muna da rubuce-rubucen magabata kuma ba z amu ce ba mu gane ba tun da ga mutane Allah ya aiko su koyar da mu, mutane su gyara halayensu domin in ba su gyara halinsu ba ko da Allah ya so da shugaba na gari sai ya dauke abin shi.

Akwai Magani Ga Kowane Kalubale Sai Dai In Ba A Yi Amfani Da Shi ba - Masana

Har wasu daga mabiya addinin Kirista sun aminta da cewa irin wadannan ayyuka da ake bayani akai suna da amfani ga rayuwar jama'a.

Da yake an jima ana fadakarwa akan koyi da ayyukan magabata don samun kyakkyawar rayuwa, yin amfani da koyarwar ka iya nuna tasirin aiki da ita ko akasin haka.

Saurari cikakken rahoto daga Muhammad Nasir:

Your browser doesn’t support HTML5

Akwai Magani Ga Kowane Kalubale Sai Dai In Ba A Yi Amfani Da Shi ba - Masana.mp3