Tsohon Gwamnan jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido, wanda hukumar EFCC, ta gurfanar a gaban kuliya ya samu an bada belinsa dangane da tuhumar da ake masa tare da ‘yayansa na yin sama da fadi da kudaden jama’a.
Ko yaya Sule Lamido, ya ga yadda ‘yan Najeriya, ke fasara wannan badakalar da kuma yadda shi kansa ya dauki halin da yasamu kansa.
Tsohon Gwamnan yace “ Na sha shiga kurkuku an daure ni amma banbanci wancan da wannan shine watakila niyyar, kasan ance dan Adam, nada farashi ukku, kowaye kai akwai gada guda ukku da bazaka iya tsallakewa ba, kodai gadan kudi ko gadan tsoratarwa ko gadan ‘ya’ya, duk shugabani a duniya idan ana so a mallakesu akan so abisu da abun duniya, idan Imanin su yayi karfi suce baza suyi ba toh sai kuma a nemi aganamasu azaba, idan wanna ya kasa faruwa sai a koma kan ‘ya’ya, toh mafi yawanci a duniya babu wanda za’a yiwa wannan taku gida ukku ya haye, idan aka zo kan ‘ya’ya dole a lokaci mutun ya karye."