Akwai Bukatar Inganta Harsunan Kasashen Afirka

Abdulkarim Muhammad

Abdulkarim Muhammad, shugaban kamfanin shirya fina-finai da aikin jarida na kamfanin Moving Imagine, ya bayyana cewar suna gab da fitar da wata gasa da zata kawo hadin kan masu shirya fina-finai a duk harsunan Afirka, don haduwa a garin Kano wajen baje kolin fina-finansu.

Wanna ya hada da tallata fina-finan nasu domin baiwa wasu harsunan Afirka damar amfana da al'adun juna tare da samar da hanyar sayar da fina-finan Afrika, maimakon sayen fina-finan turawa na waje da ake yi a yanzu.

Abdulkarim Muhammad, wanda ya bayyana haka a wata zantawa da yayi da wakiliyar DandalinVOA a hira ta mussaman, ya bayyana cewa wannan shine irinsa na farko da yake kokarin samar da hadin kan masu shirya fina-finai a Afirka tare da samar da hanyar sayar da fina-finan Afirka cikin sauki ba tare da baiwa na Turawa muhimmanci ba, kamar yadda ake yi a yanzu.

Ya kara da cewa gasar ta bada tsarin cewar duk harshen da aka fitar da fim za’a fassara shi a harshen Turanci, ko Faransanci da kuma Larabci, kuma akwai kudin shiga kadan da za’a biya.

Ya ce babban kalubalen da ke gabansa a yanzu shine ta yadda zai ja hankalin masu shirya fina-finai kuma a halin da ake ciki Moving image, ke daukar nauyin komai amma ana neman wasu kamfanoni da hukumomi domin suyi hadin gwiwa domin tabbatar da yiwar wannan gasa.

Domin cigaban duniya ya saukaka komai domin haka ne suke ganin wannan wata hanya ce da masu shirya fina-finai ke da damar isar da sakonninsu tare da inganta harsunan Afirka.

A halin dai da ake ciki an kafa wasu kwamitocin da zasu kula da tafiyar wannan gasa sannan suna gab da bude shafin yanar gizo website da za’a tallata wannan sabon kudirin.