“Ganin yadda ake fuskantar wannan mumunan bala’in da tashe-tashen hankali, ya zama dole a dauki matakan da ba-na-sabon ba”, a cewar Zeid Ra’ad Hussein.
Zeid yayi kira ga kwamitin sulhun MDD da ya dauki matakan da zasu hana mambobin kwamitin yin amfani da karfin ikon su don hana aiwatar da kudurorin kwamitin, idan akwai damuwar cewa an aikata laifukan yaki, lafukan da suka saba hakkokin bil’adama ko kuma an yi kisan kare dangi.
Mambobin kwamitin sulhun su biyar na da karfin ikon hawa kujerar naki. Cikinsu har da Rasha kawar Siriyya, da China wadda ta hana a dauki wasu matakai akan gwamnatin Siriyya tun farkon rikicin a watan Maris a shekarar 2011.
Amurka ma na da wannan ikon. Sai dai goyon bayan ta ga yan tawaye dake adawa da shugaba Assad ya sa ta a wani bangare dabam na rikicin da Rasha, wanda ya sa kasashen biyu hurawa bangarorin biyu da ke fada wuta akan kulla yarjejeniya samar da zaman lafiya da kuma tsagaita wuta lokuta dayawa a baya.