Shugaban Amurka mai barin ado Barack Obama yace nan bada jimawa ba sabon shugaban da zai gaje shi, Donald Trump zai gane cewa akwai banbancin tsakanin suruttai ba kakkautawa a lokacin yakin neman zabe, da wainar da ake toyawa da zaran mutum ya hau kan karagar mulkin shugabancin Amurka.
A haduwarsa da manema labarai jiya, wacce kuma itace ta farko tun gagarumar nasara mai ban mamaki da Trump ya samu a zaben da aka yi a makon jiya, shugaba Obama yace yana jin Trump zai zame hazikin shugaba muddin yana tareda mutanen kirki a zagaye da shi.
Shugaba Obama yace zai bar Amurka cikin kyakyawan hali nagari fiyeda yadda ya same ta, kuma yana da karfin imanin cewa Trump zai aiwatarda manufofi masu anfani.
A jiyan ne kuma shugaba Obama ya bar Amurka a tafiyarsa ta karshe a wa’adin mulkinsa, inda zai ziyarci kasashen Girka, Jamus da kuma Peru.