Akwai Alamun Jam'iyyar Shugaba Macron Zata Samu Rinjaye

Emmanuel Macron a rumfar zabe

Masu zabe a Faransa suna kada kuri’unsu yau lahadi a zagaye na karshe na zaben ‘yan majalisar dokokin kasar.

Masu fashin baki sun ce zata yiwu masu jefa kuri’a su ba sabon shugaba Emmanuel Macron gagarumar nasara, watakila ma jam’iyyarsa ta samu kujeru fiye da 400 a majalisar mai kujeru 577. Wannan zai ba Macron mai ra’ayin tsaka tsaki damar ganin an aiwatar da alkawuran da yayi na kawo gyara a dokokin kwadago masu tsauri da tsarin kula da marasa galihu.

A bayan shekaru biyar na mulkin jam’iyyar gurguzu, inda tsohon shugaba Francois Hollande ya kasa cimma gurinsa na rage rashin aikin yi tare da bunkasa tattalin arziki, Faransawa sun nuna damuwa sosai.

Amma ganin yadda sabon shugaban nasu ya karbu yanzu haka idon duniya, ya kara zaburar da su. Firayim minister Edouard Phillipe yace ana daukar Macron a zaman ma’ajin amana da kwazo.