Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Djibouti Ta Mika Kuka Ga Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya


Kasar Djibouti ta zargi makwabciyarta Eritrea da laifin mamaye wani yankin baki iyaka da suke gardama a kai, a bayan da Daular Qatar ta janye sojojin kiyaye zaman lafiyarta daga nan a cikin makon nan.

Jami’an gwamnatin Djibouti sun ce sojojin Eritrea sun mamaye Dutsen Dumeira da tsibirin Dumeira a ranar larabar da ta shige, kwana guda bayan da Qatar ta janye sojojinta su 450, wadanda suka shafe shekaru 7 suna rike da wuraren biyu.

Qatar ba ta bayyana dalilin janye sojojin kiyaye zaman lafiyarta ba, amma kuma yin hakan ya biyo bayan furucin da Djibouti da Eritrea suka yi na nuna goyon baya ga kasar Sa’udiyya a rikicin diflomasiyyar da take yi da Qatar.

Jakadan Djibouti a MDD, Mohammed Siad Doualeh, ya fadawa VOA cewa kasarsa ta mika kuka ga Kwamitin Sulhun majalisar.

Kungiyar Tarayyar Kasashen Afirka ta yi rokon da a kwantar da hankula a kai zuciya nesa, ta kuma fada cikin wata sanarwa cewa tana shirin tura tawagar masu bincike zuwa bakin iyakar Djibouti da Eritrea.

VOA ta tuntubi jami’an gwamnatin kasar Eritrea domin jin ta bakinsu game da wannan lamarin amma har yanzu basu ce uffan ba.

Sojojin kasashen biyu sun ba hammata iska na tsawon kwanaki 4 a watan Yunin 2008 a bayan da Djibouti ta ce Eritrea ta tsallako iyaka ta girka sojojinta.

Qatar ta gabatar da tayin shiga tsakanin a wannan rikicin a 2010, kuma kasashen biyu sun yarda a kan Qatar ta gurka sojojinta suyi aikin kiyaye zaman lafiya a yankin da suke gardamar mallakarsa. Amma har ya zuwa yau ba a dauki matakin da aka yi alkawari na gabatar da batun gaban kotu domin sasantawa ba.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG