Yayin da 'yan Najeriya ke cigaba da nuna damuwa bisa dokar biyan tsofaffin gwamnoni da shugabanin majalisun dokokin kasar kudaden fansho da alawus alawus na mussaman na miliyoyin Naira.
Jihar Akwa-Ibom da ke yankin Naija Delta, na daya daga cikin wadanda tsoffin gwamnoni da mataimakansu suke karbar makudan kudade, bisa wata doka da majalisar dokokin jihar ta samar a shekarun baya.
Ita dai wannan doka ta yiwa duk wani tsohon gwamna da mataimakinshi tanadin cewa a duk shekara yana da Naira miliyan dari biyu (N200,000,000.00) da sabuwar mota guda biyu da masu yi musu hidimar gida da kuma tanadin samar musu da cikakken tsaro.
Sauran tanade tanadan sun hada da samar musu da mai dafa musu abinci da direba da kuma tabbatar da cewa ana kula da lafiyarsu da ta iyalansu, kuma kan kula da lafiyar tasu za’a basu Naira miliyan dari (N100,000,000.00) a duk shekara.
Sannan har ila yau za’a gina musu katafaran gida mai daki biyar a Abuja babban birni tarayyar kasar da kuma jihar ta Akwa-Ibom.
Wannan batu dai ya janyo ce-ce kuce a jihar ta Akwa-Ibom, da al'umma a jihar suka bayyana cewa bai dace ba, ganin yadda tsoffin gwamnoni suke karbar makudan kudade a duk shekara, inda suka ce harkokin lafiya, ilimi, dai sauransu duk sun lalace ga kuma dumbin bashi da ake karbowa a jihar da kuma kasar.
Tun a baya, wata kotun daukaka kara ta bada wani hukunci akan irin dokokin da majalisun dokokin jihohi suke yi cewa ya sabawa kundin tsarin mulki kasar.
Saurari cikakken rahoton wakilinmu Lamido Abubakar:
Your browser doesn’t support HTML5