Akshay Kumar Ya Sake Jan kaya

Akshay Kumar Bollywood

Fim din Akshay Kumar Toilet Ek Prem Katha, da ya fito a makon da ta shige ya baiwa marada kunya a Bollywood ta kasar Indiya.

Shi dai fim din an sa ran cewa zai samarda kimanin dalar Amurka miliyan shida da dubu dari hudu ($6.4M) ne amma sai fim din ya samarda fiye da nunki biyu inda ya samarda fiye da dalar Amurka miliyan goma sha biyar($15M).

Shi dai wannan fim din ya kasance na soyayya ne kuma ya samu gogaggun da suka gabatar da shi kamara yadda ya kamata kuma gashi yana da nishadantarwa da gamsarwa daga farko har karshen fim din.

Daga dukkan alamu fim din kwalliya zata biya kudin sabulu, domin fim din ya kasance daya daga cikin fina finan da suka jawowa Bollywood jama’a da kuma makudan kudaden shiga kamar yadda fim din Akshay Kumar na baya Jolly LLB 2, yayi.

Your browser doesn’t support HTML5

Akshay Kumar Ya Sake Jan kaya - 2'00"