Akalla Soja Guda Ne Ya Mutu A Hadarin Jirgin Saman Da Ya Auku A Abuja

Jirage biyu samfurin F7 sun yi hadari a yayin atusaye a Abuja. Matuka jiragen sun yi nasarar tsira ta hanyar saukar lema amma guda ya rigamu gidan gaskiya a cewar kakakin rundunar sojojin saman Najeriya, Air Commander Ibikunle Daramola.

A kwanan nan, jiragen saman rundunar sojin Najeriya ke ta yin atusayen gwaji gabanin shirye-shiryen bikin ranar 1 ga watan Oktoba wato na murnar zagayowar ranar samun 'yancin kan Najeriya.

"Jirgin F7 gudunsa ya zarce gudun kara ko murya," inji Wing Kwamanda Musa Isa Salman. A saboda tsananin gudun da yake da shi, kuma iri biyu ne, da trainer da kuma fighter wato na yaki. Jirgin trainer ya banbanta da na fighter domin yana daukan mutane biyu wanda hakan ke bayar da daman amfani da shi wajen koyarwa amma na fighter mutum guda yake iya dauka.

Sai dai har yanzu ba a tabbatar ba ko fighter ko trainer ne suka yi hadari ba.

"Tun da dai jirgi biyu ne kuma suna maganar matuka uku, to duk yadda aka yi kila ko trainers guda biyu ne ko kuma fighters," inji Wing Kwamandan.

A cewar wani tsohon kwamanda a rundunar sojin saman Najeriya, Air Kwamanda Baba Gamawa ya ce faruwar wannan hadarin za a iya cewa kaddara ce kawai idan aka yi la'akkari da taka-tsantsan da sojin ke yi musamman ga jiragen yaki.

"Dalili kuwa shine wadannan jirage ana kula da su kuma matuka jirgin na samun horaswa iya gwargwado sannan ana basu kulawa."

Muna jiran sauran karin bayani daga rundunar sojin saman Najeriya dangane da wannan hadari.

Saurari cikakken rohoton Hassan Maina Kaina

Your browser doesn’t support HTML5

Hadarin Jirgin Soja A Abuja - 2' 32"