Aisha Buhari Ta Gargadi Iyaye Su Hana 'Ya'yansu Fada A Ranar Zabe

Matar Shugaban Kasa Aisha Buhari

Uwargidan mataimakin shugaban Najeriya, Dolakpo Osinbajo ta gargadi al’ummar Najeriya da su fito kwansu da kwarkwatansu don gudanar da zabe a zabubbukan da za’a gudanar a kasar.

Madam Dolakpo Osinbajo ta bayyana hakan ne a wurin gangamin yakin neman zaben jami’iyyar APC da aka shiryawa mata da matasa a shiyyar jihohin tsakiyar Najeriya da aka gudanar a garin Lafia, babban birnin jahar Nasarawa.

Uwargidan mataimakin shugaban kasar wacce ta wakilci matar shugaban kasa, Hajiya A’isha Buhari ta zayyana ayyukan ci gaba da shugaba Muhammadu Buhari ya yiwa yara da mata da suka hada da shirin ciyar da ‘yan makarantar firamare kyauta wanda ya baiwa mata ayyukan yi, da tallafin kudi wa kananan ‘yan kasuwa da ake wa lakabi da Trader Moni da bayyana tabbacin kowa zai fita daga kangin talauci.

Da take magana da yawun uwargidan shugaban kasar A’isha Buhari, Dolakpo Osinbajo tace kada iyaye su kyale ‘ya’yansu su yi fada a lokacin zabe, sai dais u kada kuri’arsu su je gida su jira sakamakon zabe.

Ministan inganta wasanni da matasa yana cikin kusoshin jami’iyar APC da suka halarci taron, ya kuma ce gwamnatinsu ta yi rawar gani dalili kenan da suke bukata a sake zabenta. Yace an samu ci gaba a gyarar hanyoyi da tsaro da ma tattalin arzikin da saransu.

Ga rahoton Zainab Babaji a wurin taron gangamin a Nasarawa:

Your browser doesn’t support HTML5

Taron Gangamin APC A Nasarawa