'Yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a hari ta sama da aka kai birnin Sana'a a watan Yuli, sun ce ba su da halin sake gina gidajensu.
Wadanda suka tsira da rayukansu bayan hari ta sama da aka kai a wata unguwar bakar fata a birnin Sana'a watannin baya, suna hako tarkacen gine-gine.
Makwabtan unguwar bakar fatar da gidajen su suka ruguje a wajen birnin Sana'a na kallon barnar da aka yi.
Wadannan mutanen sun yi tafiyar kusan kilomita daya don neman ruwa a birnin Sana'a.
Ba za a iya gyara gidajen da suka lalace sanadiyar hari ta sama da aka kai a Yemen ba. Harin dai an kai shi ne a wata unguwar da mafi yawancinsu bakar fata ne a birnin Sana'a, cikin watan Yuli.