Aikin Sake Gina Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya Zai Ci Naira Tiriliyan 31 – Hukumar NEDC

Taron hukumar raya yankin arewa maso gabashin Najeriya NEDC

Hukumar raya yankin arewa maso gabashin Najeriya NEDC ta ce za a kashe kudi dala Biliyan 80 a gagarumin tsarinta na shekaru 10, don aikin sake gina yankin tare da fitar da al’umomin daga kangin talauci.

Hukumar NEDC ta ce wannan gaggarumin tsarin na daga cikin bukatun shugaban Najeriya, na ganin an farfado da jihohin yankin arewa maso gabashin kasar, da ya fuskanci koma baya sakamakon aiyukan mayakan kungiyar Boko Haram.

Yankin arewa maso gabas ya hada da jihohin Adamwa da Bauchi da Borno da kuma Yobe. Yanzu haka hukumar NEDC ta hada kai da masu ruwa da tsaki wajen bincike a kananan hukumomi 121 da ke yankin, a wani mataki na gano hanyoyin da za a bi don cimma wannan manufa.

Taron hukumar raya yankin arewa maso gabashin Najeriya NEDC

Hukumar NEDC ta ce tsarin ya kunshi shirye-shirye sama da 500 wadanda za su inganta tare da saukaka ayyukan ci gaban na zahiri da zamantakewar shiyyar da aka ware shekaru 10 don aiwatar da aikin zuwa 2030.

Gwamnar jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa tsarin zai matukar rage wahallahum da mutanan yankin ke fuskantar la’akari da irin ayyukan da aka sa a gaba.

An kiyasta kashe kudin aiwatar da aikin kan kimanin dala biliyan 80, wanda yake kwatankwacin Naira Tiriliyan 31.01 ake sa ran samu daga hadin gwiwar masu ruwa da tsaki da kungiyoyi da kuma kamfanoni masu zaman kansu na ciki da wajen kasar.

Domin Karin bayani saurari rahotan Shamsiyya Hamza Ibrahim:

Your browser doesn’t support HTML5

Aikin Sake Gina Yankin Arewa Maso Gabashin Najeriya Zai Ci Naira Tiriliyan 31 – Hukumar NEDC - 3'18"