Kwararru a fannin harkokin kare hakin bil’adama daga kasashen nahiyar Afrika 44 sun kushewa karuwar gasawa wadanda ake tuhuma da ayyukan ta’addanci akuba a hannun ‘yan sanda, ko cibiyoyin binciken sojoji da kuma cibiyoyin sarautar gargajiya kamar gidajen fada.
A karshen taron kwanaki uku da aka kamala jiya Jumma’a, kwararru sun yi kira ga shugabannin kasashen nahiyar Afrika dake fuskantar wannan matsalar, su yi tsayin daka wajen ganin jami’an tsaro suna kiyaye dokokin kasa da kasa da suka jibinci kare hakkin bil’adama.
Kasashen Afrika suna fama da ayyukan ta’addanci cikin shekarun nan.
Kwararru kan harkokin kare hakkin bil’adama da suka halarci taron basu bayyana kasashen da suka fi keta hakin bil’adama ba. Sai dai sun kushewa dokokin da aka kafa bara a kasashen Kamaru da Chadi, kasashen da suke fama da hare haren kungiyar Boko haram,da suka kafa dokar aiwatar da hukumcin kisa kan wadanda aka samu da laifin ayyukan ta’addanci. Kwararrun sun kuma ce sojoji a kasashen Afrika da suke fama da hare haren ta’addanci, suna gasawa wadanda ake zargi da ayyukan ta’adanci akuba, su kuma wulakanta su.
Ranar goma ga watan Disamba shekara ta alib da dari tara da tamanin da hudu.