'Yan Afirka Ta Kudu Su Na Murna Da Alfaharin Zuwan Gasar Cin Kofin Duniya A Kasarsu

‘Yan wasan tamaula na Afirka ta Kudu sun ce karawar farko da zasu yi da kasar Mexico a lokacin bude wannan gasa ranar jumma’a, ita ce tamaula mafi muhimmanci da zasu taba bugawa a rayuwarsu

Shekaru shida a bayan da Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya, FIFA, ta bayar da sanarwar cewa kasar Afirka ta Kudu ce zata dauki nauyin gasar cin kofin duniya ta 2010, al’ummar kasar su na cike da farin ciki da kuma alfahari yayin da ake shirye-shiryen karshe na bude wannan wasa jibi Jumma’a a birnin Johannesburg.

Masu shirya wannan gasa sun ce sun kimtsa domin gasar cin kofin duniya na farko da za a gudanar a nahiyar Afirka.

‘Yan wasan tamaula na Afirka ta Kudu sun ce karawar farko da zasu yi da kasar Mexico a lokacin bude wannan gasa ranar jumma’a, ita ce tamaula mafi muhimmanci da zasu taba bugawa a rayuwarsu.

Afirka ta Kudu tana fata cewa daukar nauyin gasar cin kofin duniya zata taimaka wajen kawar da mummunan kallon da ake ma kasar tun zamanin mulkin wariyar launin fata.

Ana sa ran cewa ‘yan kallo fiye da dubu casa'in zasu makare filin wasan Soccer City na Johannesburg domin bude wannan gasa da za a yi.

Wannan gasa ta cin kofin duniya ta kawo sabbin filayen wasanni a Afirka ta Kudu yayin da aka gyara wadanda ake da su. Haka kuma an bunkasa cibiyoyin sufuri, aka gina sabbin layukan jiragen kasa, ciki harda layin dohgo na jirgin kasa mai matukar sauri na farko a nahiyar Afirka. An gina sabbin hanyoyi, aka gyara na da, yayin da aka fadada filayen jiragen sama aka gina wasu domin dimbin jama’ar da zata halarci wannan gasa.