Afghanitsan: Amurka, Taliban Sun Kammala Tattaunawa

Mambobin kungiyar Taliban a zaman tattaunawar da aka yi a Doha, babban birnin Qatar

An kammala zaman da aka kwashe kwanaki 9 ana yin sa a Qatar da goshin Asuba a yau Litinin, a cewar wani dan kungiyar ta Taliban.

Amurka da kungiyar Taliban sun kammala tattaunawar da suke yi a zama na takwas da zimmar cimma matsaya tsakaninsu domin kawo karshen yakin da ake yi tun shekaru 18 da suka gabata a Afghanistan domin share fagen tattaunawar zaman lafiya a tsakanin 'ya'yan kungiyar.

An kammala zaman da aka kwashe kwanaki 9 ana yin sa a Qatar ne da misalin goshin Asuba a yau Litinin, a cewar wani dan kungiyar ta Taliban.

An ci gaba da zaman ne a jiya da al’umar Musulmi a duk fadin duniya suka fara shagulgulan Sallah wanda za a kwashe kwanaki uku ana yi, wato Eid al- Adha.

A wani takaitattacen jawabi, Zabihulla Mujahid ya ce, tattaunawar tana da “sarkakiya kuma tana tasiri” domin duka bagarorin biyu sun amince su tuntubi jagororinsu saboda abin da zai biyo baya.