Kungiyar Taliban ta ce tana fatan a yau Lahadi za a kammala tattaunawar da take yi da Amurka, wacce za ta ba da damar a cimma matsaya kan yadda za a kawo karshen yakin Afghanistan da aka kwashe shekaru 18 ana yi.
Zaman tattaunawan tsakanin bangarorin biyu da ke takaddama, wanda ake yin shi a karo na tara, ya gudana ne a inda aka saba yin taron, wato kasar Qatar da ke yankin tekun Fasha.
Tawagar Amurka ta samu jagorancin jami’in diplomasiyya Zalmay Khalilzad, wanda ba’amurke ne dan asalin kasar ta Afghanistan.
A jiya Asabar, kakakin Taliban Zabihulla Mujahid, ya fadawa Muryar Amurka cewa, bangarorin biyu suna kokarin shata yadda dakarun da Amurka ke jagoranta za su janye daga kasar ta Afghanistan.