Kasar Afghanistan na sa ran samun ganimar jiragen sama masu saukar ungula kamar guda 200 da wasu nau’in jiragen na sama na daban a matsayin wani bangaren shiri na shekaru hudu na inganta matakan tsaron kasar don yakar ‘yan Taliban, a cewar Dawlat Waziri, wani mai magana da yawun ma’aikatar tsaron Afghanistan.
Dawlat ya ce tattaunawa akan shirin na cikin abubuwan da wakilan Amurka da ake sa ran zasu kai ziyara Kabul kwanan nan zasu tattauna idan sun isa can.
Gabanin ziyarar, mai bada shawara ta fuskar tsaro a Afghanistan Haneef Atmar yayi wata zantawar sa’a daya ta bidiyo, a yau Laraba da takwaransa na Amurka Herbert Raymond McMaster akan batun hadin guywar tsaro tsakanin kasashen biyu.
Wannan shine karo na farko da manyan jami’an gwamnatin Amurka zasu kai ziyar Kabul tun bayan da aka sami sabuwar gwamanti a kasar, kuma zasu tattauna akan yadda Amurka zata cigaba da bada taimako ga Afghanistan, a cewar shugaban majalissar dokokin Afghanisatn Abdul Raouf Ibrahim.