Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shirin Fitar Burtaniyya Daga Tarayyar Turai Ya Kankama


Babi na 50 na yarjejeniyar tarayyar turai ya tanadi yadda wata kasa dake membar kungiyar ballewa.

Shirin da Kasar Burtaniyya ke yi na ficewa daga tarayyar turai ya kankama bayan da firayin ministar Burtaniyya Theresa May ta soma daukar matakin aiwatarda abubuwan dake kunshe a cikin abinda ake kira “Babi na 50” na yarjejeniyar kungiyar, wanda kuma shine ke nuna an soma tattaunawar da za’a share har shekaru 2 ana yi akan yadda za’a tsinke dangatakar fiyeda shekaru 40 dake tsakanin Ingila da kungiyar ta Tarayyar Turai.

Babi na 50 na yarjejeniyar kasancewa cikin tarayyar ta turai ya tanadi yadda wata kasa dake cikin kungiyar zata iya fita daga tarayyar.

Kokarin Biritaniya na ballewa daga tarayyar turan dai ya faro ne a watan Yunin shekarar 2016 a lokacin da ‘yan kasar suka jefa kuri’a akan batun. Sakamakon kuri’ar ya nuna yadda mutanen Buritaniyya ke dada janyewa daga amincewa da mulkin rikau da kuma bayyana tunanin yadda ‘yan kasar ke nuna jin takaicin yadda tsarin shugabancin tarayyar ta Turai yake tauyewa dan Burtaniyya ‘yancinsa ta hanyoyi da dama.

Kuri’ar jin ra’ayin da aka kada ta kuma janyo murabus din tsohon firayin minista David Cameron, wanda a lokacin yakin neman zabensa karo na biyu, yayi alkawarin shirya wannan kuri’ar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG