AFCON: Najeriya Ta Kammala Wasanninta Ba Tare Da Shan Kaye Ba

Victor Osimhen (Hoto: Instagram Victor Osimhen)

Dan wasan tsakiya na kungiyar Napoli, Victor Osimhen ne ya fara zura kwallo kafin a je hutun rabin lokaci.

‘Yan wasan Super Eagles na Najeriya sun kara zama daram a gurbin da suka samu a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON bayan da ta lallasa ‘yan wasan Crocodiles na kasar Lesotho da ci 3-0.

Najeriya ta riga ta samu gurbi tun bayan da kasar Saliyo da Lesothon suka tashi canjaras a wasan da suka yi a karshen makon da ya gabata.

Wannan nasara da Najeriya ta samu a ranar Talata a filin wasa na Teslim Balogun da ke Legas, ta sa ta kammala yakin neman shiga gasar ba tare da an sha ta a wani wasa ba a rukunin L, inda ta kare da maki 14.

Najeriya ta buga wasannin shida kenan.

Dan wasan tsakiya na kungiyar Napoli, Victor Osimhen ne ya fara zura kwallo kafin a je hutun rabin lokaci.

Sannan sai Oghenekaro Etabo da Paul Onuachu suka kara kwallaye dai-dai bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

Shi dai Onuachu ya shigo ne a matsayin dan wasan canji, wannan kuma ita ce kwallonsa ta biyu a tsakanin wasannin biyu da Najeriya ta buga a kwanan nan.

Shi ne ya ci kwallon da Najeriya ta yi nasara a wasanta da Jamhuriyar Benin inda aka tashi da ci 1-0.

Masu sharhi a fannin wasan kwallon kafa na cewa, abin da ya ragewa Najeriya a yanzu shi ne, ta maimaita irin wadannan nasarori da ta samu a gasar ta AFCON, wacce za a fara a watan Janairun 2022 a kasar Kamaru.