Dan tsaron bayan Najeriya, WIlliam Troost Ekong, ne ya zura wa Najeriya kwallo ta bugun fenariti.
Washington DC —
‘Yan wasan Najeriya sun doke Kwaddebuwa, masu karban bakuncin gasar nahiyar Afirka ta AFCON.
Wasan, wadda ita ce na biyu da Najeriya ta buga a gasar, ya tashi 1-0.
Dan tsaron bayan Najeriya WIlliam Troost Ekong ne ya zura wa Najeriya kwallo ta bugun fenariti.
Saura minti 5 a cika awa daya da fafatawa a wassan ne Troost Ekong ya zura.
Najeriya na na biyu akan teburin 'Rukunin A' bayan ta tashi kunnen doki a wasarta ta farko da Equitorial Guinea.