Wannan martani na zuwa sa'o'i kadan a take wasan dab da na karshe na gasar AFCON tsakanin manyan kungiyoyin kwallon kafar Afrika, inda kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya zata kara da takwararta Bafana-Bafana ta Afrika ta Kudu.
DIRCO ta ce kalamun na Ofishin Jakadancin Najeriya a Afirka ta Kudu bai yi mata dadi ba, ganin cewa ansha karawa tsakanin kungiyoyin kwallon kafar biyu amma ba'a taba samun wata hatsaniya ba.
Ta kuma kara da cewa, kasar Afirka ta Kudu, kasa ce dake da masoya kwallon kafa da yawa, ta kuma yi kira da Ofisoshin Jakadancin kasashe da nan gaba su tuntube su idan har bukatar diflomasiya ta taso.
Hamza Abdullahi, wani dan Najeriya ne dake karatu a Afirka ta Kudu ya bayyana cewa akwai fahimtar juna da kuma mutunta juna tsakaninsu da yan Afirka ta Kudu duk cewa ansha samun hatsaniya a baya.
Shi ma Nuhu Abba Ibrahim, tsohon jami'in shige da fice ne a Najeriya, wanda kuma ya taba zama a Afirka ta Kudu, ya shaida cewa akwai dangantaka me karfi tsakanin yan Afirka ta Kudu da kuma yan Najeriya mazauna can.
A hirarsa da Murya Amurka, Faruk Bibi Faruk, me sharhi ne kan lamuran da suka shafi yau da kullum, kuma Malami a Jami'ar Abuja, ya ce "ba wannan hanya yakamata Ofishin Jakadanci Najeriya ya bi wajen yiwa ƴan kasarta gargadi ba, domin hakan kamar ciwa ita kasar Afirka ta Kudu fuska ne a idon duniya".
A jiya ne Ofishin Jakadanci Najeriya dake Afirka ta Kudu ya shawarci ‘yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu da suyi kaffa-kaffa wajen bikin murna idan har Super Eagle tayi nasara akan Bafana-Bafana ta Afirka ta Kudu, wanda hakan bai yi wa Afirka ta Kudun dadi ba.
Yanzu dai magoya bayan kungiyar kwallon kafan kasashen biyu suna jiran dakon yadda wasan zata kaya.
A saurari cikakken rahoton Rukaiya Basha:
Your browser doesn’t support HTML5