Ado Bayero: 1930 - 2014

Alhaji Ado Bayero

​Rahotanni dake fitowa daga birnin Kano a arewacin Najeriya sun tabbatar da rasuwar Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero da safiyar Juma’ar nan.
“Mai martaba Sarki, lokacinsa yayi, kuma gaskiya ne, Allah Ya karba abunsa,” Walin Kano, Alhaji Mahe Bashir Wali kennan wanda ya tabbatar da rasuwar marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero da safiyar Juma’arnnan.

A shekara ta 1963 ne marigayi Alhaji Ado Bayero ya hau kan karagar sarautar Kano, kuma a shekarar 2013 ne ya cika shekaru 50 akan mulki.

Tuni dai jama’ar Kano, da sauran sassan Najeriya ke cigaba da bayyana alhini dangane da rasuwar Sarkin Kano.

Wani dan Kano, Sani Ibrahim Yusuf cewa yayi “wannan abu na jimami ne sosai ga duk al-ummar Musulmi, ba ma iya mutanen da cikin garin Kano ba.”

Shaibu Isa daga Kano yace wannan ba karamin babban rashi bane.

“Gaskiya wannan rashi da muka yi sai dai muyi fatan Allah Ya gafartawa mai martaba, kuma Allah Ya bamu wanda yafi shi adalci.”

Daga cikin kalaman da sarkin yayi a lokacin da ya cika shekaru 50 akan mulki, cewa yayi “jama’a shekara kwana ce, domin yau mun cika shekaru 50 inda Allah Yayi mana baiwa da alfarmarsa inda ya damka mana sarautar Kano.”

Sarkin dai ya rasu yana da shekaru 84 a duniya.

Your browser doesn’t support HTML5

Sarki Ado Bayero Ya Rasu - 4'34"