Biyar kuma sun mutu a fafutukar daukar kayayyakin da ke cikin rumbun na ajiya.
Wani ma'aikacin asibitin kwararu ta jihar Adamawa ya tabbatar da kawo musu gawarwakin wadanda suka mutu sakamakon wanna turmutsitsin tare da sharadin sakaya sunan sa.
Kakakin Rudunar 'yan sandan jihar Adamawan SP Sulaiman Yaya Nguroje ya tabbatar da aukuwar lamarin a hedkwatar 'yan sandan jihar.
DR Adamu Babikwai, mai sharhi ne kan al'amuran yau da kullun a jihar Adamawa kuma malami a kwalejin horas da malamai ta gwamnatin tarayya da ke Yola, ya yi kira ga iyayen yara da su ja wa 'ya'yansu kunne su bi doka a jihar Adamawa.
Ya kara da cewa "su kuwa gwamnatin su rika gaugautawa wajen rabawa al'umma abin da ya zama hakkokinsu a matsayinsu na y'an kasa."
Wannan arangamar ce ta sa gwamnatin jihar Adamawa ta ayyana dokar ta baci ta sa'o'i ashirin da hudu a duk fadin jihar, sanarwan sakataren yada labaran gwamnan jihar Mr humonshi Wunosiko ya sanya wa hannu.
Yanzu haka dai komai a jihar Adamawa ya daidaita a jihar.
Sarari rahoton Salisu Lado a sauti:
Your browser doesn’t support HTML5