Adamawa: ‘Yan Gudun Hijira Sun Koka Kan Rashin Samun Kulawa

ADAMAWA: 'Yan gudun hijira da za'a rufe sansaninsu

Yanzu haka yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya raba da gidaje dake sansanonin da aka tanadar a jihar Adamawa na kokawa game da rashin kulawar da suke zargin ana nuna musu ta fuskacin cimaka da abubuwan more rayuwa.

Duk da cewa wasu sun koma yankunansu, kawo yanzu akwai yan gudun hijira da dama da rikicin Boko Haram ta raba da gidaje da yanzu haka ke sansanin da aka tanadar a wasu kananan hukumomin jihar Adamawa.

Kuma su dai wadannan yan gudun hijiran yanzu haka dai na kokawa game da halin da suke ciki na karancin abinci da ababen more rayuwa, lamarin da ya kai wasun su fita suna kwadago, domin neman abun sakawa a baka.

A watannin baya, baya ga tallafin hukumomin bada agaji suma yan aikin sakai na kungiyoyi masu zaman kansu kan kawo nasu tallafin, to amma yanzu lamarin ba haka yake ba, batun da kwamared Ahmad Gambo Daud na cibiyar kare hakkin dan Adam ta Centre for Human rights advocacy ke ganin akwai abun dubawa.

To wai ko me hukumar bada agaji ta NEMA da ke kula da sansanonin yan gudun hijiran ke yi ne game da halin da suke ciki yanzu? Imam Abbani Garki, shine jami'in hukumar mai kula da jihohin Adamawa, da Taraba, ya ce matsalar jinkirin bada ofishinsu na Yola bane kamar yadda wasu ke tunani.

Dubban rayuka ne dai suka salwanta sakamakon tashe tashen hankula na Boko Haram baya ga wasu dubban da aka tilastawa gudun hijira a wannan rikici da aka shafe fiye da shekaru bakwai ana fama.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Adamawa: ‘Yan Gudun Hijira Sun Koka Kan Rashin Samun Kulawa - 4'01"