Adamawa: ‘Yan Banga Sun Sami Horo Daga ‘Yan Sanda

Yan Banga Na Samun Horo Daga Yan Sandan Jahar Adamawa

Jami’an ‘yan sandan jahar Adamawa sun horas da matasa ‘yan aikin sa kai na ‘yan Banga 251, domin samun dabarun aiki da bayanai a cikin al’umma.

Matasan dai sun fito ne daga jahohin Adamawa da Taraba, an kuma horas da su a filin horas da ‘yan sandan kwantar da tarzoma shiyya ta 14 dake Yola.

AC Aminu Tuta ‘daya daga cikin shugabanin yan Banga a jahar Adamawa, ya yaba da irin horon da suka samu daga jami’an yan sandan. Kuma yayi alkawarin zasu baiwa ‘yan sandan jahar hadin kai ‘dari bisa ‘dari domin a samu hanyar shawo kan matsalar tsaro da ake fuskanta.

Shima da yake karin haske game da matakan da suke dauka don kaucewa bata gari Mustafa Bashar, dake zama jami’in mulki na kungiyar yan sakai ya ce akwai matakan da suke dauka wajen daukar sabbin ‘yan Banga, domin fidda dan duma daga kabewa.

Masu fashin baki na ganin akwai bukatar matasa su dinga shiga ire-iren kungiyoyi na ‘yan sa kai, musamman a wannan lokaci na rashin aikin yi ga matasa.

Wannan yunkuri na zuwa ne yayin da gwamnatin jahar Adamawa ke tallafawa ‘yan aikin sa kai na Maharba da yan Bangan dake taimakawa a yankunan Madagali, wato ‘yan Gombi Boys, domin samun nasarar kakkabe sauran ‘yan kungiyar Boko Haram da suka rage, kamar yadda kwamishinan yada labaran jahar Adamawa Ahmad Sajo ya tabbatar.

Domin karin bayani ga rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Adamawa: ‘Yan Banga Sun Sami Horo Daga ‘Yan Sanda - 3'24"