Babban batun da ya dauki hankalin mutane shi ne na wani kalamun da aka ji aka kuma yada a kafofin labarai da gwamnan jihar yayi ta wayar tarho.
A cikin kalamun nasa gwamnan yana barazanar kashe wasu jami'an zabe wadanda suke kokarin karya alkawarin da yace sun yi masa akan zabukan. Kalamun nasa suna kuma yiwa lamarin tsaro barazana a jihar da kuma kasa gaba daya.
Dangane da hakan ne babban sifeton 'yansandan Najeriya Ibrahim Idris ya nada wani babban kwamiti wanda zai binciki al'amarin.
Tuni mutanen da aka nada suka fara tuntubar daya daga cikin manyan kanfunan sadarwa na kasar domin yanka sashen maganganun da gwamnan yayi domin cigaba da bincike.
Baicin binciken kalamun kwamitin zai cigaba da binciken wasu matsaloli na tsaro, musamman wadanda suka kusa kasara zabukan da aka gudanar a jihar ta Rivers.
A cikin kalamun da gwamnan yayi an jishi yana cewa zai kashe jami'an zaben idan basu cika alkawarin da suka yi ba ko kuma su mayar masa da kudin da ya basu.
Wani da aka jikata yace wasu suka yi masu diran mikiya a kauyensu da bindigogi suka ta yin harbe harbe kana suka yi anfani da adda suka sassareshi suka kuma kashe abokinsa.
Ga rahoton Lamido Abubakar da karin bayani.