Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari ya dakatar da sakataren gwamnatin kasar Babachir David Lawan da darakta Janar na hukumar leken asirin Nigeria, NIA, Ambassador Ayo Oke kan zargin almundahana da kudaden gwamnati.
Wannan kuma na zuwa ne yayin da rikicin jam’iyar APC dake mukin jihar ke kara zafi a tsakanin yan bangare su Babachur, da kuma yan bangaren gwamnan jihar Bindo Umaru Jibrilla dake tare da tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar.
Domin yayin da yan bangaren tayi dadi, ke murna da dakatarwar da aka yi, yanzu haka su kuwa wasu kusoshin jam’iyar APC dake bangaren Abuja, wato bangaren su Babachur Lawan, na nuna yatsa ne ga yan daya bangaren da cewa daman sun san a rina.
To sai dai kuma wasu masu sharhi na ganin cewa dakatar da sakataren gwamnatin Najeriya, Babachir David Lawal, da kuma shugaban hukumar leken asirin kasar (NIA) Ambasada Ayo Oke da shugaba Muhammadu Buhari ya yi na nuni da yadda shugaban ya fara sauya takunsa ayanzu ko da yake akwai bukatar sake duba cikin gida, yayin da wasu ke cewa an yi fargar jaji.
Yanzu dai yan Najeriya sun zura ido ne don ganin yadda zata kaya, yayin da kwamitin bincike karkashin jagorancin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ke haramar fara aiki domin gano gaskiyar zargin da aka yi wa Babachir na amfani da mukaminsa domin samun kudi ta hanyar da ba ta dace ba.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul'aziz.
Your browser doesn’t support HTML5