Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga-zangar Kin Jinin ‘Yan Majalisun Dattawan Najeriya


Daruruwan Matasa Masu Zanga-zanga A Jihar Neja
Daruruwan Matasa Masu Zanga-zanga A Jihar Neja

Daruruwan matasa masu goyon bayan jam’iyyar APC sun gudanar da zanga-zangar nuna rashin jin dadinsu ga ‘yan Majalisun Dattawan Najeriya, akan zaman doya da manja dake tsakaninsu da fadar shugaban ‘kasar Najeriya.

Masu zanga-zangar sun mamaye ofishin shugaban kwamitin shari’a na Majalisar Dattawan Sanata David Umaru, dake Minna fadar gwamnatin jihar Neja. Inda suka bayyana cewa taru ne domin nuna bacin ran su ga ‘yan Majalisar.

Shugaban tawagar matasan kwamrad Nuraddeen Iliyasu, ya ce sun taru ne domin nuna fushinsu da kuma bacin ran su game da irin wakilcin da ‘yan Majalisun su ke yi musu.

Matasan dai sunce matakin da za su ‘dauka gaba shine shirya yadda zasu fara kiranyen ‘yan Majalisun da suka zaba su wakilce su, su kuma sake zaben wasu shugabannin da suke ganin za su yi musu wakilci na gari.

Daga baya Sanata David Umaru ya kira taron manema labarai domin mayar da martani, inda ya ce su kam suna tare da shugaban kasa Mohammadu Buhari dari bisa dari.

Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG