A zaman kotun da ya cika da magoya bayan tsohon gwamnan, babban lauyan Najeriya Sam Olugunorisa, (SAN) ya shaidawa kotun cewa tun bayan kai shi jarun, lafiyar tsohon gwamnan ke kara tabarbarewa wanda a dalilin haka ne suka bukaci a bashi beli domin ya je a duba lafiyarsa.
Haka nan ma kuma a zaman kotun an mika wata wasikar da hukumar kula da gidajen yari a jihar suka rubuta game da tabarbarewar lafiyar tsohon gwamnan Bala Ngillari, inda a wasikar dake dauke da sa hannun mataimakin kwanturolan gidajen yarin jihar Adamawan, Mr John Bukar ya rattabawa hannu, an bayyana cewa hawan jinin tsohon gwamnan jihar Adamawan ya karu zuwa 200 daga 100 yayin da ciwon sugarsa kuma ya karu zuwa 160.
To sai dai kuma, an yi doguwar jayayya a tsakanin lauyan tsohon gwamnan da na bangaren hukumar EFCC, Abubakar Aliyu, game da batun bada belin, amma kuma a karshe alkalin kotun mai shari’a Nathan Musa, ya amince da bada belin akan kudi Naira Miliyan dari tare da masu tsaya masa mutum biyu da zasu mika takardun gidajensu.
Magoya bayan tsohon gwamnan irinsu Hon. Abdullahi Prembe, tsohon kwamishinan yada labarai a zamanin Ngillarin, ya bayyana farin cikinsu da cewa zasu cigaba da neman hakkinsu.
Ita ma jam’iyar PDP, ta yaba da matakin bada belin da kotun ta yi, kamar yadda Barr.A.T Shehu, sakataren wani bangare na jam’iyar PDP a jihar yace suna farin ciki.
A ranar Litinin shida ga wannan wata na maris ne tsohon Gwamnan jihar Adamawan James Bala Ingilari, ya zamo tsohon gwamna na biyu a tarihi da aka daure kan aikata laifukan da suka shafi cin hanci da rashawa, kuma baya ga Ngillari, yanzu haka akwai wasu tsoffin gwamnonin jihar biyu dake gaban kuliya bisa laifukan cin hanci da watanda da dukiyar jihar.
Daga Yola, ga Ibrahim Abdul’aziz da Karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5