Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Ma'aikata da Gwamnan Taraba Sun Shiga Wata Takunsaka


Gwamnan Taraba Architect Darius Ishaku
Gwamnan Taraba Architect Darius Ishaku

Yanzu haka an soma kai ruwa rana a tsakanin kungiyoyin ma’aikata da kuma gwamnan jihar Taraba Akitet Darius Dickson Isiyaku sakamakon sanarwar da gwamnan yayi na hana duk wani ma’aikaci yin bori ko zanga-zangar neman hakki,batun da shugabanin kwadago a jihar ke cewa ba zata sabu ba,wai bindiga a ruwa.

Tun a makon jiya ne dai aka soma kai ruwa rana a tsakanin gwamnatin jihar Taraban da kuma kungiyoyin kwadago a jihar lamarin da ya kai daliban makarantun firamare fitowa kan titi suna zanga-zanagar lumana don nemawa malanasu hakkinsu abun da gwqamnatin ta kira zugawar 'yan adawa

A sanarwar gargadi da gwamnan jihar Arch.Darius Isiyaku ya fitar ta hannun na’ibin sakataren yada labaransa Mr Iliya Bekyu ya gargadi yan kwadago a jihar da cewa gwamnatin jihar ta haramta duk wani jerin gwano ko zanga-zanga da ma’aikata zasu yi domin neman hakkokinsu. Yan bukatar su nemi yin anfani da hanyar tattaunawa

Wanda a don haka ne sanarwar ta yi kira ga iyaye da kada su bari wasu su yi amfani da yayansu don fitowa wajen jerin gwano da zummar nemawa ma’aikata hakkinsu.

To sai dai a martanin da shugabanin kwadago a jihar su ka maida,yan kwadagon sun yi tir da Allah wadai da wannan sanarwa ta gwamnatin jihar.

Mr Peter Gambo dake zama shugaban kungiyar kwadago a jihar ya shaidawa Muryar Amurka cewa su ko a gyalensu da abun da ya kira barazanar da gwamnatin jihar keyi musu a yanzu.

Tuni dai wannan mataki na hana ma’aikata bori ya soma jawo cece-kuce a jihar inda yan rajin kare hakkin dan Adam da kuma lauyoyi suka soma maida martani.

Barrister Idris Jalo shine shugaban kwamitin kare hakkin dan Adam na kungiyar lauyoyin jihar Taraban yace akwai abun dubawa.

Yanzu dai an zura ido a ga yadda zata kaya a tsakanin ma’aikatan jihar da kuma gwamnatin jihar dake haramar karbar nata kason na tallafin Paris-Club daga gwamnatin tarayya.

Ibrahim Abdulaziz nada karin bayani a wannan rahoton.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG