Kasancewar jahar Adamawa na daga cikin jahohin da matsalar rikicin Boko Haram ya fi shafa a Arewa maso Gabashin Najeriya, hakan yasa hukumomi ke gargadin mutanen da ke komawa garuruwansu da su rika sa ido musamman a wannan lokaci na bikin Kirsimeti.
Wannan kuwa na zuwa ne a dai dai lokacin da dakarun Najeriya ke cewa suna samun nasarar karkabe burbudin mayakan Boko Haram din daga dajin Sambisa, wanda hakan yasa hukumomin tsaro ke daukan matakan kare rayuka da kuma dukiyar jama’a musamman a yankunan da aka fara komawa.
Da yake karin haske kan matakan da suke dauka a yanzu, Kwamishinan yada labarai na Jahar Ahmad Sajo, yace cikin matakan da sojoji ke dauka shine sun ware wani sashe a Madagali, inda suke ce duk wanda ke cikin sashen zasu iya tabbatar masa da tsaro amma duk wanda ya fita yana saka kansa cikin matsala.
Haka kuma sun gargadi al’umma da cewa duk wanda zasu tafi gona kar suyi sammako, a jiya har sai rana ta fito inda za a hadu da sojoji da ‘yan Banda domin basu tsaro.
Shima da yake tsokaci Mr Adamu Kamale, ‘dan Majalisar wakilai mai wakiltar Madagali da kuma Michika, yankunan dake fama da hare-haren sari ka noke daga yan Boko Haram, yace har yanzu suna cikin halin zaman fargaba.
Tuni dai aka ayyana ranakun Litinin da Talata a matsayin ranakun hutu inda gwamnan jahar Adamawa Sanata Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla, ke kira ga matafiya su bude ido su kula.
Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.
Your browser doesn’t support HTML5