A ranar Talatar da ta gabata ne wasu kungiyoyin matasan Arewa suka shaida wa manema labarai cewa sun gaji da korace-korace da gutsuri-tsoma daga kungiyoyin matasan kabilar Igbo masu neman kafa kasar Biafra a kudu maso gabashin kasar inda ma suka dibar musu wa’adin ficewa daga yankin arewacin kasar,batun da yanzu haka ke cigaba da jawo martani.
Baya dai ga martanin da kungiyar gwamnonin arewa ta yi,suma wasu kungiyoyi sun bi sahu wajen yin tur da wannan barazana da cewa ba za ta sabu ba wai bindiga a ruwa.
Da take maida nata martani hadakar kungiyar kawo fahimtar juna ta matasan arewa,wato Northern Youth For Peace and Reconcilation Forum ta bakin shugaban kungiyar Hon.Hussaini Gambo Bello tace su basu yarda da ko yan arewa ne ke wannan barazana ba.
Suma dai al’umman Mummuye,sun nuna bacin ransu da cewa kamata yayi da a kai zuciya nesa. Mallam Aliyu Tukur Binkola dake zama jakadan Mummuye,yace lokaci yayi da matasan Najeriya zasu yi karatun ta-natsu,don kaucewa yan ingiza mai kantu ruwa,da burinsu shine raba kan kasar.
To sai dai ga masu fashin baki irinsu Mallam Yakubu Musa ,yace duk da cewa kalaman na matasan arewan bai dace ba,to amma idan aka bi ta barawo to ya kamata abi ta mabi sawu.
Yakubu Musa yace idan za’a tuhumi wadannan kungiyoyin matasa to ai kamata kuma suma yan daya bangaren dake irin wannan barazana a bincike su.
Batun kafa kasar Biafra dai na ci gaba da tayar da jijiyoyin wuya a tsakanin al'ummar Najeriya , inda aka samu bullar kungiyar matasan Igbo ta IPOB karkashin jagorancin Nnamdi Kanu,wanda a kwanaki nema wata babbar kotu ta bayar da belin Mista Kanun bayan tsare shi bisa zargin cin amanar kasa.
Su dai yan kungiyar ta IPOB na fafutikar ganin an gudanar da kuri'ar raba-gardama ne kan batun kafa kasar ta Biafra,batun dam asana ke ganin dole ayi taka-tsantsan ganin abun da yakin basasa ya jawo.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5