ADAMAWA: Al’ummar Unguwar Modire Sun Koka Kan Rashin Ababen More Rayuwa

Yadda ake Sufirin kaya saboda rashin kyauwu hanya

Wasu al’ummomin arewa maso gabashin Nijeriya na fama da mastalar ingancin rayuwa, musamman abin da ya shafi ilimi da kiwon lafiya, kamar yadda wasu daga cikin mazauna yankin Modire de ke karamar hukumar Yola ta kudu a jihar Adamawa suka koka. 

A hirar shi da Muryar Amurka,Malam Usman Modire, e mai unguwar Modire, ya ce tunda su ke rayuwa a wannan unguwar basu da hanya mai kyau, ba asibiti, ba wutar lantarki, da dai sauran ababen more rayuwa, unguwar dai ba ta wuce kilomita biyu daga fadar jihar ba.

Shi ma Alhaji Abdurazak Koronko, mazauni a wannan yankin, ya tabbatar da cewa mata masu juna biyu sun sha haihuwa a kan titi a cikin keken a-daidaita-sahu sakamakon rashin hanya mai kyau a wannan yanki. A saboda haka, suna kira ga gwamnatin jihar da ta taimaka a kawo musu dauki a yankin nasu.

To ko gwamnatin jihar Adamawa zata yi da gane da wannan lamari da ya shafi al’umar wannan unguwar ta Modire? Honarabul Abdullah Adamu Prambe, wanda ke zaman kwamishinan raya karkara da ci gaban al’umma na jihar Adamawa, ya ce yaje unguwar da kansa don ganin halin da jama’a suke ciki kuma zasu dauki matakin da ya ce, amma yace alu’mmar wannan yankin su kara hakuri saboda irin yanayi na aikin gwamnati.

Saurari cikakken rahoton Salisu Muhammed Garba:

Your browser doesn’t support HTML5

Al’ummar Unguwar Modire A Karamar Hukumar Yola Sun Koka Kan Rashin Ababen More Rayuwa