Adadin ‘Yan wasan Real Madrid Da Suka Kamu Da COVID Ya Kai Takwas

Tawagar 'yan wasan kungiyar Real Madrid

Kungiyar ta Real Madrid ta ce dukkan ‘yan wasan takwas ba za su buga karawar kungiyar da Athletico Bilbao ba a wannan Laraba.

‘Yan wasan Real Madrid David Alaba da Isco Alarcon sun shiga jerin ‘yan wasan kungiyar da suka kamu da cutar COVID-19.

Hakan na nufin adadin ‘yan wasan da suke takawa kungiyar leda a jerin farko da suka harbu da cutar ya kai takwas.

Alaba wanda mai tsaron baya ne da Alarcon mai taka leda a tsakiya sun bi sahun Luka Modric, Marco Asensio, Rodgyro, Gareth Bale, Marcelo da mai tsaron raga na biyu Andriy Lunin.

Kungiyar ta Real Madrid ta ce dukkan ‘yan wasan ba za su buga karawar kungiyar da Athletico Bilbao ba a wannan Laraba.

Ita ma Bilbao za ta buga wasan ba tare da ‘yan wasa hudu ba, ciki har da mai tsaron raga Unai Simon da mai tsaron baya Inigo Martinez