Adadin Wadanda Suka Mutu Sanadin Rikicin Sudan Ya Zarta 600 – Hukumar WHO

'Yan Sudan sun nemi mafaka a Chadi

Hukumar lafiya ta duniya ta WHO ta ce adadin wadanda suka mutu sakamakon mummunan fadan da aka shafe kusan wata guda ana yi a Sudan ya zarce 600.

A ranar Talata hukumar WHO ta Majalisar Dinkin Duniya ta fadi cewa mutane fiye da 5,000 ne suka jikkata sakamakon fadan tsakanin sojojin Sudan a karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan, da kuma dakarun RSF a karkashin jagorancin Janar Mohammed Hamdan Dagalo.

Janar-janar din biyu abokai ne a baya, wadanda suka hada kai wajen kitsa juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Oktoban shekarar 2021, lamarin da ya kawo cikas ga shirin mika mulki ga farar hula bayan hambarar da shugaba Omar al-Bashir a shekarar 2019.

Shugaban Sudan Umar al-Bashir

An samu takaddama tsakanin janar-janar din ne game da yadda ya kamata a hade dakarun RSF da sojojin kasar da kuma batun wanda wa ya kamata ya kula da wannan shirin. Yi wa rundunar sojan kasar garambawul na daga cikin kokarin maida mulki ga farar hula da kuma kawo karshen rikicin siyasar da ya haifar da juyin mulkin da sojoji suka yi a shekarar 2021.

Yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin bangarorin biyu ta kasa kawo karshen rikicin ko ma ta taimaka wajen sassauta shi.

Burhan da Daglo

Wakilan bangarorin biyu da ke fada sun shafe kwanaki suna ganawa a birnin Jeddah na kasar Saudiyya domin cimma yarjejeniyar bada damar kai agajin jinkai ga dubban mutanen da ke bukatar abinci, matsugunni da kuma jinya a Khartoum da sauran garuruwan Sudan.

Tuni dai Masarautar Saudiyya ta yi alkawarin bai wa Sudan tallafin dala miliyan 100.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da ‘yan Sudan 700,000 ne suka tsere daga gidajensu tun bayan barkewar rikici a watan Afirilu, adadin da ya linka fiye da 334,000 da hukumar ta bayar da rahoton cewa sun kaurace wa matsugunnansu a makon da ya gabata.