An sake samun wani da ya mutu da cutar Ebola a Congo, abinda ya kai adadin wadanda cutar ta kashe zuwa goma sha biyu, bisa ga cewar ma’aikatar lafiya ta Damokaradiyar Jamhuriyar Kwango.
Rasuwar ta auku ne a kauyen Iboko dake arewa maso yammacin lardin Equater.
Ma’aikatar lafiya tace akwai kuma wadansu mutane hudu da ake kyautata zaton sun kamu da cutar a lardin. Yanzu haka an tabbatar mutane talatin da biyar sun kamu da cutar ta Ebola a kasar Kwango.
Gobe litinin za a fara allurer rigakafin cutar Ebola a kauyukan Bikoro da Iboko dake lardin Equateur. Ana kuma shirin rigakafi a Mbandaka, babban birnin lardin mai mutane miliyan daya da dubu dari biyu, dake bakin kogin Kwango, inda aka tabbatar da mutane hudu sun kamu da cutar.