Adadin Wadanda Suka Ji Rauni A Harin Santa Fe Ya Karu

Wataq mace da danta a makarantar Santa Fe

Yayinda al’ummar Santa Fe, a jihar Texas ke jimamin harin kan mai uwa da wabin da aka kai da ya yi sanadin mutuwar mutane goma, galibi dalibai a makarantar sakandare, Jami’ai sun kara adadin mutanen da suka ji raunuka zuwa goma sha uku.

Jami’an jihar Texas sun tuhumi wani matashi dan shekaru goma sha bakwai da aikata kisan kai, sakamakon harbin da ya janyo asarar rayuka a makarantar sakandare ta Santa Fe.

Dalibai sunce dan bindigan, wanda jami’an tsaro suka bayyana da suna Dimitrios Pagourtzis wanda yake kusa da ajin karshe a makaranta, ya bude wuta da misalin karfe takwas na safe ranar jumma’a a makarantar sakandaren Santa Fe.

Gwamnan jihar Texas Greg Abbott yace ‘yan sanda sun gano ababan fashewa da irin kwalbar da ake amfani da ita a wajen tarwatsa wuta a gidan maharin, da kuma cikin wata mota da aka ajiye kusa da makarantar sakandaren da aka kai harin, an kuma tsinci wadansu ababan fashe fashe a harabar makarantar

Abbot yace dan bindigar da ake zargi da kai harin da ya sallama ‘yancinsa na kin Magana da jami’an tsaro, yace da farko yayi niyar kashe kansa bayanda ya kai harin, amma ya shaidawa jami’an tsaro da aka kamashi cewa, bashi da karfin halin kashe kansa.