Adadin Wadanda COVID-19 Ta Kashe a Duniya Ya Doshi Miliyan Daya

Kasashen Duniya na kara dosar adadin mace-mace sakamakon cutar COVID-19 miliyan 1, a cewar cibiyar samar da bayanan coronavirus ta Johns Hopkins da safiyar Litinin 28 ga watan Satumba.

Cibiyar ta Hopkins ta ce sama da mutane miliyan talatin da uku a duniya ne suka kamu da COVID-19.

Wani Bincike da gidan talabijin din CNN yayi akan alkaluman na cibiyar Hopkins, ya nuna cewa adadin wadanda suka harbu da cutar COVID-19 ya karu da akalla kashi goma cikin dari daga makon da ya gabata zuwa yanzu a jihohin Amurka 21.

Dr. Chris Murray, darektan cibiyar sa ido kan alkaluman harkokin Lafiya, da Nazari a jami'ar Washington, ya fada wa CNN cewa "hasashen samun karuwar masu kamuwa da cutar coronavirus a watan Oktoba a Amurka, ana sa ran zai kai har zuwa watanin Nuwamba da Disamba.

A Amurka an samu mutum fiye da miliyan bakwai da suka kamu da COVID-19, daga nan sai India da ke bi mata da sama da mutum miliyan shida, sai kuma Brazil da ta samu kusan mutum miliyan biyar da suka kamu da cutar, a cewar alkaluman cibiyar Hopkins.

Kasashen Turai kuma na fuskantar sake barkewar cutar, abinda ya sa wasu gwamnatoci a fadin nahiyar, sake dawo da matakan kulle kan jama’a da kuma masana’antu.