Adadin rashin aikin yi na ci gaba da karuwa a Amurka, tare da karin wasu ma’aikata miliyan 3 da dubu 800 da suke neman a basu tallafin marasa aikin yi a makon da ya gabata, yayin da annobar coronavirus ke ci gaba da yin mummunar illa ga tattalin arziki mafi girma a duniya, a cewar rahoton ma’aikatar ayuka a yau Alhamis.
Sabbin wadanda suke neman tallafin ya kara adadin a cikin makonni shida zuwa miliyan 30 da dubu 300, duk kuwa da cewa wasu jihohin kalilan sun soma bude wasu harkokin kasuwanci, yayin da shugaba Donald Trump ya ke kara matsa lambar bude tattalin arzikin kasar.
Amma wasu karin miliyoyin ma’aikata na iya neman tallafin marasa aikin yi a cikin makwanni kadan nan gaba yayin da annobar ta dakatar da komai gaba daya.
Sai dai Amurka ba ta taba ganin irin wannan mataki na rasa ayyukan yi ba, da ya shafi daya daga cikin kowadanne ma’aikata 6, tun daga lokacin da aka shiga cikin matsin tattalin arziki a shekarar 1930. Yadda ake sallamar ma’aikata gaba daya duk ya share karuwar ayyukan yi da aka samu tun daga karayar tattalin arzikin shekarar 2008.
Gwamnati ta sanar jiya Laraba cewa tattalin arzikin kasar ya fadi da kashi 4.8 cikin 100 a farkon rubu’in wannan shekarar.