Adadin Masu Kamuwa Da Cutar COVID-19 a Najeriya Na Karuwa

A Najeriya, mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 sun kusan 110,000 a cewar Hukumar NCDC ta kasar.

A ranar Lahadi 17 ga watan Janairu hukumar sa ido akan cututtuka masu yaduwa ta NCDC a Najeriya ta sanar da cewa mutun 108,943 ne suka kamu da cutar COVID-19 a fadin kasar, yayin da mutun 1,420 kuma suka mutu.

Jihar Lagos ce ta fi kowacce jiha yawan wadanda suka kamu da cutar inda ta ke da adadin mutun 39,723. Sai birnin tarayya Abuja da ke da adadin mutun 14,544, daga nan kuma sai jihar Filato da ke biye da mutun 6,617.

A daren ranar Asabar kadai, an sami mutun 1,598 da suka kamu da cutar a jihohi dabam-daban na kasar.

A sanarwar da hukumar ta sanya a shafinta na yanar gizo, ta kuma ce an sallami mutun 85,367 daga asibiti bayan da suka warke.

Hukumomin lafiya da jami’an lafiya a Najeriya na ci gaba da yin kira ga ‘yan kasar da su kiyaye matakan kariya daga cutar da aka sanya kamar yin nesa-nesa da juna, da sanya kyallen rufe hanci da baki, da kuma yawan wanke hannu don dakile yaduwar cutar.