Amurka ta kai wani sabon mataki game da yadda cutar COVID-19 ke “yaduwa matuka” a yankunan karkara da birane, a cewar kwararru a fadar White House da ke sa ido akan cutar.
WASHINGTON, D.C —
Adadin masu kamuwa da cutar coronavirus na ci gaba da karuwa a wasu sassan kasar kuma jami’an lafiyar al’umma na kokarin yin aiki da gwamnoni don daukar matakai a kowacce jiha.
“Mun kai wani sabon mataki" a cewar Dr. Debrah Birx. Ta kara da cewa “abin da mu ke gani a yanzu ya sha bamban da abinda aka gani a watannin Maris da Afrilu da suka gabata. Cutar na yaduwa matuka a yankunan karkara har ma da birane.
Dr. Birx, mai kula da harkokin tsare-tsare a kwamitin yaki da cutar coronavirus, ta ce mutanen da ke zama da iyali, iyaye kakanni da sauransu a wuraren da ake fuskantar yaduwar cutar, ya kamata su sanya takunkumin rufe hanci da baki a cikin gida don kare tsofaffi ko wadanda ke fama da wata larurar rashin lafiya.